Take a fresh look at your lifestyle.

NEMA Ta Yi Hasashen Jihohi 19, Yankuna 56 Da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa

0 178

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta ce jihohi 19 da al’ummomi 56 a fadin kasar nan na iya fuskantar ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliya a cikin wannan wata.

 

Mista Ibrahim Farinloye, kodinetan hukumar ta NEMA, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Legas.

 

Farinloye ya lissafa jihohi da al’ummomi kamar haka: Delta: Aboh, Jihar Ekiti; Ado Ekiti, Jihar Ondo; Akure, Idanre, Ifon, Iju Itaogbolu, Ogbese, Owo, Owena, Ondo

 

Sauran ya ce sun hada da: Jihar Legas; Apapa, Badagry, Eti Osa, Ikeja, Ikorodu, Ikoyi, Lagos Island, Ojo Lagos, Surulere; Anambra; Atani; Ogun; Ifo, Ota, Shagamu; Jihar Nasarawa; Lafia, Wamba da Kuros Riba; Ikom, Ogoja

 

Farinloye ya kuma Jera Sunayen Yankunan Jihar Bauchi : Jamaare , Misau, Azare, Itas ,Kafin Madaki,Kari, Kirfi, Tafawa Balewa, Katagum; Jigawa; Hadejia, Miga; Jihar Osun; Ilesa, Oshogbo da Kwara; Kosubosu.

 

Sauran ya ce Zamfara; Anka, Bungudu, Gusau; Jihar Sokoto; Goronyo; Adamawa; Numan, Shelleng; Taraba: Serti; Benuwai; Ito, Katsina-Ala, Vande-Ikya; Jihar Imo: Oguta, Orlu da kuma jihar Abia; Ugba.

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *