Dakarun sojan Najeriya sunyi musayar wuta da ‘Yan ta’adda a Zungeru dake karamar hukumar Wushishi a jihar Neja , inda wasu daga cikin dakarun suka kwanta dama a kokarin su na kare martabar kasar, sakamakon haka ne babban hafsan dakarun sojan kasa Lt General Taoreed Lagbaja ya isa birnin Minna fadar gwamnatin jihar, a wani ziyarar bazata don ganawa da dakarun dake aiki a jihar, inda daga bisani ya wuce yankin da lamarin ya faru don samun cikkakkun bayanai daga bakin kwamandan 1 Division Major General Bamidele Alabi.
Da yake jawabi ga dakarun, babban hafsan dakarun sojan ya bukaci su da su kara kokari a aikin su don ganin an samar da tsaro a dukkanin fadin kasar, inda ya ce kare rayuka da dukiyoyin alummar Najeriya shine babban kudirin dakarun sojan kasar.
Lt General Taoreed Lagbaja ya Kara da cewar. ” ku Kara himma a ayyukan ku don ganin an kawar da dukkanin bata garin dake addabar kasar “
Babban hafsan dakarun sojan kasa ya kuma baiwa dakarun tabbacin gwamnatin na kara samar masu da karin kayayyakin aiki, da Kuma jami’ai domin fatattakar saura Yan ta’addan dake addabar yankin da ma wasu sassan kasar.
Nura Muhammed.
Leave a Reply