Gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da sayar da taki ga manoma a farashi mai rahusa domin Basu damar gudanar da ayyukan su na noma a dukkanin kananana hukumomi jihar 25.
A lokacin kaddamar da sayar da takin, gwamna Umar Mohammed Bago ya ce wannan wani mataki ne da gwamnatin sa ta dauka don ganin ta bunkasa harkokin noma ganin cewar mafi akasarin alummar jihar Neja manoma ne.
Tun bayan kaddamar da shirin, ‘Yan siyasa da Shugabannin gargajiya ke ta bayyana irin yadda Shirin ya sami karbuwa inda suka ce shirin wani bangare ne da zai kawo wa alummar jihar saukin damuwar da suke fama da ita, musammama manoma.
A zantawar sa da muryar Najeriya a garin Minna, Alhaji Awana Awaisu Kuta dake zama jagoran garkuwa alummar Gbage a jihar Neja ya ce wannan shirin da gwamnatin jihar Neja ta bullo dashi zai taimakawa gwamnatin a kokarin ta na samarwa da alumma cigaba a fadin jihar Neja.
Alhaji Awana Awaisu Kuta ya ce bayaga sayar da taki ga manoma cikin rahusa akwai bukatar ganin gwamnati ta samarwa manoman bashi na kudi ko Kayayyakin aikin noma irin su tarakta da sauran Kayayyakin da za su taimaka masu.
Ganin cewar mafi akasarin alummar jihar manoma ne, sai dai a yan shekarun nan wasu daga cikin yankin jihar na fama da matsalar Yan ta’adda wanda hakan ta chilastawa wasu daga cikin manoman yankin barin gonakinsu sabili da rashin tsaro.
Basaraken ya ce akwai bukatar ganin gwamnati a wannan bangaran ta himmatu wajan ganin an kawo karshen matsalar tsaro ta yadda manoma da ma sauran alumma zasu ji dadin gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali
To sai dai tun a lokacin kaddamar da shirin tallafin takin ga manoma a jawabin sa Gwamna Umar Mohammed Bago ya ce gwamnatin jihar a shirye take na ganin ta hada hannu da sauran jami’an tsaro don ganin an murkushe Yan ta’addan dake addabar jihar.
Ko baya ga wannan ma , Gwamnan ya Sha alwashin Samar da tarakta 300 da za a rabawa kananana hukumomi jihar 25 domin taimaka masu ta hanyar noman zamani.
Nura Muhammed.
Leave a Reply