Jami’an Rasha sun zargi Ukraine da kai hari da jirgin sama mara matuki kan wani gini a birnin Masko, lamarin da ya haddasa fashewar wani abu da aka ji a yankin kasuwanci na birnin.
Magajin garin Sergei Sobyanin ya ce jami’an tsaron sama sun harbo jirgin mara matuki tare da tarkacen shi da ya fada a cibiyar baje kolin birnin.
Wannan dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren da aka kai a babban birnin kasar Rasha.
Hotunan da ba a tantance ba a shafukan sada zumunta sun bayyana sun nuna kaurin hayaki da ke tashi a sararin samaniyar birnin Masko.
Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga Ukraine, amma jami’ai a Kyiv ba su taba amincewa da kaddamar da hare-hare kan wurare a birnin Masko ba.
An kai harin ne da misalin karfe 04:00 agogon GMT, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta bayyana a shafin sada Zumunta na Telegram.
Ya ce, bayan tsarin tsaron na birnin, jirgin maras matuki ya “canza hanyar shi”, inda ya fado kan wani ginin da ba na zama ba a yankin Krasnopresnenskaya , wani yanki na Masko wanda ke dauke da wasu gine-ginen Gwamnati.
Ya kara da cewa ba a samu rahoton asarar rayuka ba tun farko.
Cibiyar Expo babban wurin nuni ne da ake amfani da shi don taro da tarurruka kuma yana mai nisan kilomita 5 (mil 3.1) daga fadar gwamnati ,Kremlin.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce tarkacen ba su haifar da gobara ba, yayin da Mista Sobyanin ya ce jirgin mara matuki bai yi wata barna ba a ginin.
Har zuwa farkon wannan shekarar, Masko taba kai wa Masko Hari a yakin Ukrain ba , amma a cikin ‘yan watannin nan an kai hare-haren jiragi mara matuki.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply