Nan ba da jimawa ba kwamitin majalisar wakilai zai fara bincike kan rashin tura kudade zuwa asusun gidaje na kasa (NHF) da yadda ake amfani da asusun tun shekarar 2011.
Kwamitin ya aike da goron gayyata ga masu ruwa da tsaki domin gudanar da bincikensa wanda zai fara aiki a ranar Laraba 23 ga watan Agusta.
Shugaban kwamitin, Honarabul Dachung Musa Bagos a cikin takardar da ya aikewa manema labarai, ya ce kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ne zai kaddamar da zaman binciken.
Daga cikin masu ruwa da tsakin da aka gayyata sun hada da shugaban ma’aikatan tarayya; babban akawu na tarayya; babban mai binciken kudi na tarayya; shugaban hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka masu alaka (ICPC); Shugaban riko na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da kuma Sufeto Janar na Tarayya.
Sauran sun hada da; babban darakta/shugaban zartarwa na Babban Bankin jinginar gidaje na Najeriya; jami’in da ke kula da lamunin ci gaban ma’aikatar; manajan darakta/shugaban zartarwa na, hukumar kula da gidaje ta tarayya; babban sakataren ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa; babban sakatare na ma’aikatar ayyuka da gidaje; sakataren zartarwa, kwamitin bayar da lamuni na ma’aikatan gwamnatin tarayya; shugaba/shugaban majalisar, kungiyar masu gina gidaje ta Najeriya; dukkan ma’aikatu, sassan da hukumomi; kwamishinan inshora/babban jami’in gudanarwa, hukumar inshora ta kasa (NAICOM), sauran masu ruwa da tsaki da sauran jama’a.
Sanarwar ta kuma bukaci cibiyoyi da jami’an gwamnati da abin ya shafa da su mika takardarsu da sauran takardunsu ga sakatariyar kwamitin.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply