Kungiyar kasashen yammacin Afirka, Ecowas, ta yi watsi da sanarwar da jagoran juyin mulkin Nijar ya yi cewa ba za a iya maido da mulkin farar hula ba har tsawon shekaru uku.
Kwamishinan harkokin siyasa na kungiyar, Abdel-Fatau Musa, ya ce ba za a amince da jadawalin ba.
A ranar Asabar din da ta gabata, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce ana bukatar tattaunawa ta kasa domin kafa harsashen sabon tsarin siyasa a Nijar.
Kungiyar Ecowas ta yi barazanar daukar matakin soji don dawo da hambararren shugaban kasar.
Jama’a sun sake yin gangami a Yamai babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga juyin mulkin.
Sai dai rahotanni sun ce wasu da ke adawa da mamayar sojojin na fargabar bayyana ra’ayoyinsu a bainar jama’a
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply