A yanzu haka ana ci gaba da rantsar da Ministoci 45 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Taron dai na samun halartar shugaba Tinubu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da wasu gwamnonin jihohi.
Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda da shugaban kasar ya fitar da sunayen wadanda aka nada
An rantsar da Ministocin ne a rukuni biyar.
Rukunin farko sun hada da Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, Karamin Ministan Kwadago, Nkiru Onyejiocha, Ministan Ilimi, Tahir Mamman, Karamin Ministan Mai, Ekerikpe Ekpo da Ministan Harkokin Mata, Uju Ohaneye.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike shi ne sabon Ministan da ke kula da ma’aikatar babban birnin tarayya (FCT) sannan Festus Keyamo mai kula da ma’aikatar sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya.
Wasu ministocin sun hada da Wale Edun (Ministan Kudi da Hadin Kan Tattalin Arziki), Adegboyega Oyetola (Sufuri), David Umahi (Ayyuka) da Betta Edu (Hukumar kyautata rayuwa da Jin kan Jama’a).
Ladan Nasidi.
Leave a Reply