Take a fresh look at your lifestyle.

UNICEF TA YI ALLAH-WADAI DA HARIN DA AKA KAI A HABASHA

0 244

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya yi Allah-wadai da harin da sojojin Habasha suka kai ta sama a yankin Tigray wanda ya afkawa wata makarantar renon yara. Harin dai shi ne karo na farko da kasashen duniya suka tabbatar da cewa an kai harin ne a makarantar ‘Kindergarten’ bayan da hukumomin ‘yan tawaye suka yi ikirarin cewa wani jirgin sama ya jefa bama-bamai a wani yanki da ke Mekele.

Gwamnatin Habasha ta yi watsi da wannan zargi, inda ta dage cewa jiragen saman sojojin Habasha sun kai hari ne kawai a kan “wuraren sojoji” kuma suna zargin ‘yan tawayen da kai hare-hare. Rahoton ya ce harin ya afku ne da misalin karfe 13:00 na agogon kasar, ya kuma kai hari wata makarantar renon yara mai suna Red Kids Paradise inda ya kashe mutane hudu ciki har da yara biyu.

A ranar Larabar da ta gabata ne aka sake gwabza fada a arewacin kasar Habasha tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen Tigrai bayan an kwashe watanni biyar ana gwabza fada. Bangarorin biyu dai sun zargi juna da sake fara yakin da sanyin safiyar Larabar bayan da aka samu lalurar fada tun watan Yunin 2021. Rikicin na Tigray wanda ya fara a watan Nuwambar 2020, ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

AFRICANEWS/CO

Aliyu bello

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *