Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kara zurfafa hadin gwiwa da gidauniyar Bill & Melinda Gates shekaru 11 da suka gabata. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shuaibu ya fitar a Kano.
KU KARANTA KUMA: CBN da Bill Gates sun yi hadin gwiwa don bunkasa hada-hadar kudi a Najeriya
Yusuf ya bayyana haka ne ta bakin mataimakinsa, Aminu Gwarzo, wanda ya karbi tawagar gidauniyar. Ya ce gwamnatinsa za ta inganta fannin kiwon lafiya da kayan aiki na zamani don tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya. Ya yi kira da a samar da alluran rigakafi miliyan shida domin yakar cutar diphtheria da ta barke a jihar.
Gwamnan ya kuma nuna jin dadinsa ga gidauniyar bisa tallafin da take bayarwa a fannin kiwon lafiya sannan ya bukace ta da ta fadada sha’awarta a wasu fannoni kamar noma da kudi na zamani. Mista Jeremy Zungurana, shugaban tawagar gidauniyar ta Najeriya ya yaba da hadin gwiwar da ke daurewa da kuma kokarin jihar a fannin kiwon lafiya. Ya yi alkawarin ba da taimako mai dorewa ga shirin kamar yadda aka nema.
Ladan/NAN
Leave a Reply