Majalisar dokokin jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mutum 15 da zai binciki yadda bankuna da kamfanoni da sauran hukumomin jihar ke aika haraji ga gwamnati.
Kakakin majalisar Haruna Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da ya kaddamar da kwamitin a zaman majalisar a ranar Laraba a Dutse babban birnin jihar.
Aliyu ya bayyana sunayen ‘yan kwamitin da suka hada da Sani Isyaku (Shugaba), Lawan Muhammad (Mataimakin Shugaban) da Isyaku Ado (Sakatata).
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ibrahim Kabir, Abubakar Sadiq, Ibrahim Hamza, Isaq Tasiu, Sani Sale da Yau Ibrahim, Idris Muhammad, Ilu Abdu, Sale Baba, Ado Yakubu, Usaman Abdullahi da Aminu Sule.
A cewar Aliyu, kwamitin zai tuntubi hukumar tattara kudaden shiga ta jiha domin sanin matsayin bankuna da kamfanoni, da tabbatar da biyan haraji daga hukumomin da ke aiki a jihar tun daga farko har zuwa yau.
Kwamitin zai kuma binciki bin ka’idojin da suka shafi zamantakewar jama’a, gami da daukar ma’aikatan jihar aiki.
Ya kara da cewa kwamitin na da ikon hada kan sauran ‘yan majalisar inda ya dace don taimaka masa wajen gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
NAN
Ladan
Leave a Reply