Emmerson Mnangagwa, shugaban kasar Zimbabwe kuma shugaban jam’iyyar Zanu-PF mai mulki, ya kada kuri’arsa yayin da ake gudanar da zabe a kasar ranar Laraba.
Ya kada kuri’a ne tare da uwargidan shugaban kasa Amai Dr Auxilia Mnangagwa a makarantar firamare ta Sherwood Park da ke cikin garin Kwekwe.
Zaben shugaban kasar ya janyo ‘yan takara 11 da suka hada da shugaban kasar mai ci mai shekaru 80 kuma babban madugun ‘yan adawa, Nelson Chamisa mai shekaru 45, wanda ke jagorantar jam’iyyar Citizen’s Coalition for Change (CCC).
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply