Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben Gwamna: PDP Ta Kaddamar da Majalisar Yakin Neman Zabe A Jihar Imo

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

0 138

Jam’iyyar PDP reshen jihar Imo ta kaddamar da majalisar yakin neman zaben ta gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

 

Shugaban jam’iyyar Mista Charles Ugwu ne ya kaddamar da majalisar a Owerri babban birnin jihar Imo a ranar Talata.

 

 

Mista Charles Ugwu, shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), reshen jihar Imo.

Ugwu ya sanar da cewa majalisar kamfen din za ta sanya Ikenga Ugochinyere dan majalisar wakilai ta tarayya a matsayin Darakta-Janar da Yarima Marshal Okoroaforanyanwu a matsayin Sakatare.

 

 

Ugwu, a lokacin da yake kaddamar da majalisar yakin neman zaben, ya bukaci mambobinta da su yi kokarin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben.

 

 

“Da ikon da aka bani a matsayin shugaban babbar jam’iyyar mu ta PDP, na kaddamar da wannan tawagar yakin neman zaben dan takarar mu Sanata Samuel Anyanwu a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba,” inji shi.

 

Sanata Samuel Anyanwu, dan takarar gwamna na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Imo.

 

 

A nasa bangaren, Anyanwu, ya ce ya fito takarar Gwamna ne domin kawo karshen kashe-kashe da rashin tsaro a jihar, da gyara tsarin kiwon lafiyar jihar da dawo da martabar ma’aikata da masu karbar fansho.

 

 

Ya ce zai mayar da harkokin yawon bude ido jihar, sannan ya sa kananan hukumomi su sake yin aiki.

 

 

Ya kuma bukaci majalisar da kada ta ji tsoro, amma ta gudanar da ayyukanta na halal, kada wani mutum ko kungiya ya tsoratar da ita.

 

 

“Zan jagoranci kuma ba na jin tsoron kowa. Ina so in daina zubar da jini da wahala a cikin ƙasa. Kar a ji tsoro; Na san inda na fito.

 

“Ni ne manzonku, kuma zan jagorance ku daidai. Sunana Sama’ila. Allah ya faɗa, na kuwa ji,” inji shi.

 

 

Shi ma da yake magana, Okoroaforanyanwu, ya ce zabin da PDP ta yi na Anyanwu, wanda ya fito daga yankin Sanata Imo ta Gabas, ya fifita ka’idar adalci.

 

 

Ya ce gundumar ta mulki jihar tsawon watanni bakwai kacal tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

 

 

Okoroaforanyanwu, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) da Social Democratic Party (SDP) bi da bi, ya bukaci jama’ar Imo da su marawa Anyanwu baya domin ya dawo da martabar jihar da ta bata.

 

 

Babban abin da ya fi daukar hankali a wajen taron shi ne amincewa da Anyanwu da kungiyar agaji ta Rescue Mission, da kungiyar Sanata Rochas Okorocha, da kungiyar Destiny Organisation karkashin jagorancin Sen. Ifeanyi Araraume suka yi.

 

 

Maimuna Kassim Tukur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *