Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Zai Yi Jawabi A Zauren Majalisar Dinkin Duniya Karo Na 78

0 271

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a ranar Talata, 19 ga watan Satumba.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa shugaban na Najeriya a ziyararsa ta farko a zauren majalisar, zai yi jawabi ga shugabannin kasashen duniya a ranar 19 ga watan Satumba.

Shugaban Najeriyar zai kasance shugaban Afrika na biyar da zai gabatar da jawabi a ranar daya ga taron bisa jerin sunayen masu jawabi daga ofishin shugaban majalisar.

A cikin jerin sunayen, shugaba Tinubu ne zai kasance mai magana na 14 a cikin shugabannin 20 da aka shirya yin jawabi a rana ta farko.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, mai magana na 10, zai kasance shugaban Afrika na farko da zai yi jawabi a zaman safiya na Majalisar.

A zaman da za a yi na tsakar rana, ana sa ran shugabannin Afirka biyar za su yi jawabi a wurin taron.

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ne zai kasance shugaban Afirka na farko da zai yi jawabi a zaman na yammacin ranar, sai kuma shugaban kasar Morocco, Aziz Akhannouch da shugaban Mozambique, Filipe Nyusi.

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall ne zai kasance shugaban Afrika na biyar da zai yi jawabi a taron kuma shugaba na karshe a rana ta farko.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *