Take a fresh look at your lifestyle.

Masko Ta Fara Gudanar Da Zabe A Yankunan Ukraine Da Aka Mamaye Ba Bisa Ka’ida Ba

0 167

An fara zaɓen yanki a yankunan da Rasha ta mamaye na Ukraine yayin da hukumomi ke neman tabbatar da ikon Moscow na abin da ta kira “sababbin yankunan ta.”

 

Zaben wanda zai gudana har zuwa ranar 10 ga watan Satumba, ana gudanar da zaben a Donetsk, Luhansk, Zaporizhzhia da Kherson, yankuna hudu na Ukraine da Rasha ke ikirarin mamayewa.

 

Sai dai wani Jami’in na Ukraine ya bayyana zaben a matsayin “abin kunya.”

 

A halin da ake ciki, wani jirgin saman Ukraine mara matuki ya kai hari a wani gari a yammacin Rasha, kusa da daya daga cikin manyan tashoshin makamashin nukiliya na kasar, in ji wani jami’in Rasha a ranar Juma’a.

 

 

 

CNBC/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *