Denmark na ba wa jami’an diflomasiyyar Rasha 10 ne kawai a ofishin jakadancin na Copenhagen, wanda ya yi daidai da iyakar da aka sanya wa ofishin jakadancin Denmark a Moscow, in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Nordic.
Dole ne Rasha ta rage yawan ma’aikatanta zuwa jami’an diflomasiyya biyar da ma’aikatan gudanarwa 20 nan da ranar 29 ga Satumba, ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan gazawar Denmark wajen samar da biza ga ma’aikatan ofishin jakadancinta a Moscow duk da tsawaita tattaunawar.
“Tattaunawar ba ta haifar da sakamako ba saboda yunƙurin da Rasha ta yi na haɗa buƙatun biza ga jami’an leƙen asirin Rasha,” in ji ma’aikatar.
Ofishin jakadancin Rasha a Copenhagen bai samu nan da nan don yin sharhi ba.
A halin da ake ciki kuma, a cikin watan Afrilun 2022, Denmark ta mayar da martani ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta hanyar korar jami’an diflomasiyyar Rasha 15, wanda Moscow ta mayar da martani ta hanyar ayyana ma’aikatan ofishin jakadancin Denmark guda bakwai a babban birnin Rasha a matsayin ‘persona non grata’.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply