Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Girka Ta Ceci Bakin Haure 25 Daga Wutar Daji

1 133

Kasar Girka ta ceto wasu bakin haure 25 da suka makale a cikin wata gobarar dajin da ta shafe kusan makonni biyu tana ci a yankin Evros da ke arewa maso gabashin kasar, in ji hukumomi.

 

Gobarar daji a Evros, wadda ita ce mafi muni a Turai a wannan bazarar, ta kone kwana na 14 bayan da ta kashe akalla mutane 20, tare da lalata gidaje da rayuwa da kuma kona dazuzzuka.

 

Rahoton ya ce, sai dai daya daga cikin wadanda suka mutu a gobarar Evros, ‘yan ci-rani ne da suka tsallaka daga Turkiyya, inda suka tserewa ‘yan sanda a dajin.

 

Jiragen sama da daruruwan jami’an kashe gobara ne suka yi artabu da gobarar a dajin Dadia a daidai lokacin da iskar da ke saurin sauya sheka a ranar Juma’a.

 

Kakakin hukumar kashe gobara ta Girka Ioannis Artopoios ya ce “Yayin da suke aiki a tsakanin kauyukan Giannouli da Dadia, jami’an kashe gobara da ‘yan sanda sun gano mutane 25 tare da kai su wani wuri mai aminci.”

 

Bakin hauren dukkansu maza ne kuma sun ce sun fito ne daga kasashen Syria, Iraq, da Lebanon, an kama wani jami’in ‘yan sanda.

 

Rahoton ya ce Evros ya kasance sanannen tsallakawa cikin Tarayyar Turai ga dubban ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijira a kowace shekara.

 

A halin da ake ciki kuma, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Copernicus ta ce gobarar Evros ta kone akalla murabba’in kilomita 812.6, wanda ya fi na birnin New York mai fadin murabba’in kilomita 778.2.

 

Yayin da asusun namun daji na duniya, WWF ya ce an kona aƙalla kashi 30% na dajin Dadia-Lefkimi-Soufli da ke Girka.

 

Gobarar daji ta zama ruwan dare a yankin tekun Bahar Rum amma gwamnati ta ce tsananin bushewa, iska da zafi da masana kimiya ke dangantawa da sauyin yanayi ya sa ta yi muni a bana, lamarin da ya tilastawa dubban mutane gudun hijira.

 

Firayim Minista Kyriakos Mitsotakis ya fada a ranar Alhamis cewa Girka za ta harba jirage marasa matuka, da sanya na’urori masu auna yanayin dazuzzuka, da kuma daukar karin ma’aikata don inganta kashe gobara bayan sukar da masu fafutukar yanayi suka yi.

 

Switzerland ta ce a ranar Juma’a za ta aika da jirage masu saukar ungulu na sojoji uku da jami’ai don taimakawa wajen kashe gobara a Evros.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

One response to “Kasar Girka Ta Ceci Bakin Haure 25 Daga Wutar Daji”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *