Gwamnatin Kuros Riba ta yi kira da a hada karfi da karfe da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), don hada ayyukan kiwon lafiya na yau da kullun a cikin kula da ‘yan gudun hijira a jihar.
Kwamishinan lafiya na Kuros Riba Dr. Henry Ayuk ne ya yi wannan kiran a ranar Litinin a Calabar, lokacin da jami’an hukumar UNHCR suka kai masa ziyara.
KU KARANTA KUMA: COVID-19: UNHCR ta ba da gudummawar PPEs ga sansanin ‘yan gudun hijirar Kuros Riba
Da yake nanata bukatar samar da ingantacciyar hadin gwiwa, ya yi kira ga hukumar UNHCR da ta samar da karfin cibiyoyin kiwon lafiya na cikin gida don isar da muhimman ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan gudun hijirar Kamaru da mazaunan Cross River. A cewarsa, “Irin wannan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zai sa a hade ayyukan ‘yan gudun hijira zuwa ayyukan kiwon lafiya na yau da kullum na jihar. Haɗin kai na muhimman ayyukan kiwon lafiya na lafiyar mata da yara, HIV, tarin fuka da zazzabin cizon sauro zai ba da kwarin guiwa ga kokarin Cross River na samar da tsarin kiwon lafiya na duniya,” in ji shi.
Sai dai kwamishinan ya godewa hukumar ta UNHCR bisa gaggarumin yunkurin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a kananan hukumomin Ikom da Ogoja. Ya kara da cewa a halin yanzu gwamnati mai ci a jihar tana mayar da babban kantin sayar da magunguna don tallafawa ayyukan UNHCR.
A nasa bangaren, Dokta Earnest Ochang, Shugaban Hukumar Kula da Lafiyar Jama’a ta UNHCR a Najeriya, ya bayyana wasu nasarorin da hukumar ta samu yayin da ta hada gwiwa da kungiyar agaji ta Red Cross Society (NRCS) wajen kula da ‘yan gudun hijira a jihar. “Cross River ya kasance mai kyautatawa ‘yan gudun hijira kuma ya bude kofofinsa ga ‘yan gudun hijira. Wannan jiha kadai tana karbar sama da 56,000 daga cikin jimillar ‘yan gudun hijira 99,000 da ke Najeriya.”
Ya kuma bayyana cewa 87,000 daga cikin adadin ‘yan gudun hijirar Kamaru ne, wadanda suka samu kwanciyar hankali a Najeriya a cikin tashe-tashen hankulan siyasa a Kamaru. Ochang ya kuma jaddada bukatar gwamnatin jihar ta tallafa wa ayyukan ‘yan gudun hijira da kuma kiwon lafiya na yau da kullum ga kananan hukumomi da mazauna wurin.
Maimuna Kassim Tukur.
Leave a Reply