Take a fresh look at your lifestyle.

NATCOM Ta Karyata Sanarwar Daukar Ma’aikata 300,000

Musa Aminu, Abuja

0 137

Hukumar dakile yaduwar matsakaita da kananun makamai ta Najeriya wato NATCOM a takaice ta karyata labaren daukan ma’aikata dubu Dari uku da wasu ke yadawa.

Mai rikon mukamin Shugaban hukumar Dakta Baba Muhammad ya bayyana cewa labarin daukan dubban ma’aikata da wasu ke yadawa babu kamshin gaskiya ko kadan a cikinsa, hasalima tuni hukumar ta dakatar da masu yada irin wannan ikirari sakamakon rashin da’a da Kuma samun su da wasu laifuka da suka Saba ka’dojinta a don haka yanzu hukumar bata ma san da zamansu ba.

Kazalika, hukumar ta NATCOM ta bukaci Yan kasa da su yi taka tsan-tsan da irin wadannann mutane domin yanzu bata kai ga fara daukan aiki ba, amma da zarar lokaci ya yi za a ji sanarwa daga gareta a hukumance.

Babban jagoran Natcom na kasa a Najeriya ya ci gaba da cewa “ban ji dadin yadda wasu ke ci gaba da karbar kudade daga hannun masu neman aiki ba, Inka duba tuni muka bayyana Karara cewa mun dakatatar da a su”.
A cewar sa, hakan baya cikin tsarin hukumar NATCOMhasalima tuni suka samar da wani tsari na samar da kudaden shiga ga gwamnati maimakon dogaro a kanta kacokan da zarar ta fara aiki gadan-gadan.

Dr Baba Muhammad ya bukaci al’umar Najeriya da su gaggauta Kai rahoton duk wani dake neman na goro ko Kuma gudanar da wani rashin gaskiya da sunan hukumar zuwa ofishinta dake Abuja babban birnin Najeriya ko Kuma ofishin jami’an tsaro Mafi kusa domin daukan matakin da ya dace.

Ya Kuma yabawa shugaban Najeriya Bola Tinubu bisa matakan da yake dauka wajen saita al’amura a kasar.

 

Abdulkarim Rabiu

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *