Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da wasu sabbin makarantu guda uku da cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya gina a cikin kwanaki 100 na ci gaba da wa’adin shi na biyu.
Sanata Shettima ya fara aiki da makarantar Shuwari II Mega Primary School wacce ke da ajujuwa 20 masu daukar akalla dalibai 1,200.
Makarantar kuma tana da wuraren shakatawa na ma’aikata da wuraren wasanni.
Mataimakin shugaban kasar ya kaddamar da cibiyar kula da lafiya matakin farko mai gadaje 30 a Shuwari II.
An gina ta ne domin magance karuwar bukatu na kiwon lafiya sakamakon kwararowar ‘yan gudun hijira a cikin birnin Maiduguri da kewaye.
Mataimakin shugaban kasa Shettima ya kuma kaddamar da makarantar Government Day Secondary School, Gamboru, wacce aka sanya wa sunan marigayi SSG na Borno, Usman Jidda Shuwa.
Makarantar tana da ajujuwa 30, wuraren wasanni, dakunan gwaje-gwaje da sauran kayan aiki.
Ya bude wata makarantar mega a unguwar Alakaramti mai dauke da ajujuwa 30, block na gudanarwa, wuraren wasanni, wutar lantarki da tsarin ruwa.
A wuraren da aka kaddamar da aikin, mataimakin shugaban kasa ya raba riguna, kayan rubutu da litattafai ga dalibai.
Daga nan ne mataimakin shugaban kasar ya kai ziyarar ban girma ga Shehun Borno, Alhaji Dr. Abubakar Garbai Al-Amin Elkanemi a fadar sa.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply