Take a fresh look at your lifestyle.

MATAIMAKIN SHUGABAN KASA OSINBAJO YA GANA DA SHUGABAN BANKIN DUNIYA

0 330

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban bankin duniya David Malpass a birnin Washington DC, inda mataimakin shugaban kasar ya je domin tallata shirin mika wutar lantarki a Najeriya tare da masu ruwa da tsaki.

 

“Abin farin ciki ne saduwa da Shugaba @DavidMalpassWBG.

 

“Mun tattauna game da ETP na Najeriya, jajircewarmu na rashin tsaka tsaki na carbon, ci gaban Najeriya tare da burinmu na yanayi, karfafa cibiyoyin makamashi da kasuwa, jawo FDIs da kuma hada kan musayar kudi.”

 

“Na yi farin cikin jin shirye-shiryen kungiyar Bankin Duniya na tallafawa Najeriya ta wasu bangarori da suka hada da kara taimakon al’umma ga talakawa da marasa galihu,” in ji mataimakin shugaban kasa Osinbajo.

 

 

Image

Farfesa Osinbajo ya kuma ce ya gana da sakataren baitul malin Amurka J. Yellen, “domin neman goyon bayan shirin mika wutar lantarki a Najeriya da kuma shigar Najeriya a matsayin kasar G7 Climate Partnership Country.”

 

LADAN NASIDI

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *