Take a fresh look at your lifestyle.

Dan Takarar Firayim Ministan Senegal Ya Zabi FaraMinista Shi A Zaben 2024

Maimuna Kassim Tukur.Abuja.

0 65

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya zabi firaministan shi Amadou Ba a hukumance ba, a matsayin dan takarar da zai wakilci jam’iyyar shi a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Fabrairun shekara mai zuwa 2024. Fadar shugaban kasa da hadin gwiwar gwamnati ne suka bayar da wannan muhimmiyar sanarwa.

 

 

Shugaba Sall, wanda ke kan karagar mulki tun shekarar 2012, kuma ya tabbatar da sake tsayawa takara a shekarar 2019, ya bayyana a watan Yuli cewa, ba zai sake tsayawa takara karo na uku ba, ta yadda zai magance matsalolin tsarin mulkin kasar.

 

 

Saboda haka, jam’iyyar shi ta ba shi ikon zabar wanda yake so.

 

 

Amadou Ba, mai shekaru 62, ya kasance firayim minista tun watan Satumban 2022, kuma ana yi masa kallon daya daga cikin wadanda ke kan gaba a cikin ‘yan takara kusan goma da aka ayyana a cikin jam’iyyar ta shugaban kasa wadanda ke da nufin maye gurbin Shugaba Sall.

 

 

Gamayyar gwamnatin Benno Bokk Yakaar, ta bayyana zabin da suka zaba a shafukan sada zumunta, inda ta ayyana Ba a matsayin zabin da ya dace don samun nasara a zagayen farko.

 

 

Nadin Amadou Ba ya samu amincewar a hukumance yayin taron shugabannin kawancen da aka gudanar a fadar shugaban kasa, wanda aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na kasar.

 

 

Africanews/ Maimuna Kassim Tukur,Abuja..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *