Take a fresh look at your lifestyle.

Kim Jong Un Zai Ziyarci Rasha Domin Tattaunawa Da Putin

0 85

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai ziyarci Rasha domin ganawa da shugaba Vladimir Putin kamar yadda kasashen biyu suka tabbatar a ranar Litinin.

 

 

Kim zai ziyarci Rasha a cikin kwanaki masu zuwa bisa gayyatar Putin, in ji Kremlin, yayin da kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa KCNA ya ce su biyu za su ” gana kuma za su tattauna “, ba tare da yin karin haske ba.

 

 

Jami’an Amurka sun ce mutanen biyu za su tattauna yiwuwar cinikin makamai don taimakawa yakin da Rasha ke yi a Ukraine da kuma samar wa Koriya ta Arewa tsarin tattalin arziki da siyasa da take bukata.

 

 

Duk da musantawa da Pyongyang da Moscow suka yi, Amurka ta ce ana ci gaba da tattaunawa da Koriya ta Arewa don samar da makamai ga kasar Rasha wacce ta kashe makamai masu tarin yawa a cikin sama da watanni 18 na yaki a Ukraine.

 

 

Kafofin yada labaran Koriya ta Kudu sun ruwaito a ranar Litinin din da ta gabata cewa, shugaban na Koriya ta Arewa ya tashi ne a cikin wani jirgin kasa na musamman da zai nufi kasar Rasha, inda ya ambato wasu majiyoyin gwamnatin kasar da ba a bayyana sunayensu ba, sai dai nan take Moscow ko Pyongyang ba su tabbatar da takamaiman jadawalin ziyarar ba.

 

 

Koriya ta Arewa na daya daga cikin kasashe kalilan da suka fito karara sun goyi bayan Rasha tun bayan mamayar kasar Ukraine a bara, kuma Putin ya yi alkawarin fadada alakar kasashen biyu ta kowace fuska ta hanyar hada karfi da karfe.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *