Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya bayyana a ranar Asabar cewa, Amurka ta gabatar da wani sabon salon shawarwarin zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha wanda zai hada da wakilan Amurka da na Turai.
Ya yi nuni da cewa, Kyiv za ta yanke shawarar ko za ta amince da wannan tsari bayan tantance sakamakon sabunta shawarwarin da aka yi tsakanin kasashen biyu da wakilan Amurka, wanda aka koma ranar da ta gabata Juma’a.
Zelenskiy ya ce Amurka na shirin yin tattaunawa daban-daban da jami’an Rasha tare da ba da shawarar samar da wani tsari mai fadi wanda zai hada da Ukraine, Amurka, Rasha, da wakilan Turai.
Ya kara da cewa yana da niyyar tattaunawa da babban mai shiga tsakani na Ukraine, Rustem Umerov. Ana sa ran wakilan Amurka za su gana da jami’an Rasha a Florida ranar Asabar.
Ukraine da Rasha ba su yi wata tattaunawa kai tsaye ba tun watan Yuli, amma aikin diflomasiyya da ke samun goyon bayan Amurka ya karu a cikin ‘yan makonnin nan yayin da ake ci gaba da kokarin kawo karshen yakin kusan shekaru hudu.
A ranar Juma’a jami’an Ukraine da na Turai sun gana da takwarorinsu na Amurka inda suka amince da ci gaba da tattaunawa, a cewar Umerov.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos