Take a fresh look at your lifestyle.

Za’a Sasanta Bangarorin PDP Nan Ba Da Jimawa Ba – Saraki

82

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Dr Bukola Saraki, ya ce ana ci gaba da kokarin sasanta bangarorin biyu na jam’iyyar PDP.

A cewarsa, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da bangarorin jam’iyyar biyu kan yadda za a shawo kan rikicin.

Saraki ya yi wannan jawabi ne a taron matasa da jam’iyyar PDP reshen jihar Kwara ta shirya a Ilorin, babban birnin jihar, domin murnar cikar Saraki shekaru 63.

“An ci gaba da tafiya tare da kokarin daidaita bangarorin biyu, kamar yadda nake magana da ku, bangarorin biyu na jam’iyyar PDP suna ganawa da INEC, shi ke nuna muku al’amura sun fara faruwa, don haka ina so in tabbatar muku cewa nan gaba ta yi haske sosai, ina so ku yi naku bangaren.

“Yau (Juma’a) ita ce ranar zagayowar ranar haihuwata, mu yi alkawari za mu yi aiki tukuru don ganin mun kai wa jam’iyyar PDP, na gaya muku cewa ba ni da wani mukami, ku je ku kawo wadanda za su wakilce mu, mu shigo da su, mu hada kai domin samar da jihar Kwara da Najeriya, na san za mu iya yin ta tare.

“Ina tabbatar muku da cewa nan da ‘yan watanni masu zuwa, za mu zama jam’iyya daya wadda ba za ta iya rabuwa da su ba, a lokacin za mu hada bangarorin waje guda.

 

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.