Take a fresh look at your lifestyle.

Amurka Da Ukraine Na Yi Shawarwarin Tsagaita Wuta A Berlin

34

Tawagogin Amurka da Ukraine na shirin tattaunawa kan tsagaita wuta a Ukraine, gabanin wani taron koli da shugabannin kasashen Turai da shugaban kasar Volodymyr Zelenskiy a birnin Berlin ranar Litinin Mai zuwa.

Wani jami’in Amurka ya ce, wakilin shugaban Amurka Donald Trump Steve Witkoff da surukinsa Jared Kushner na tafiya Jamus domin tattaunawa da ‘yan Ukraine da Turai.

Fadar White House ta ce a ranar Alhamis Trump zai aika da jami’in tattaunawa ne kawai idan yana jin akwai isassun ci gaba da za a iya samu.

A yau litinin, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, ke karbar bakuncin Zelenskiy da shugabannin kasashen Turai a wani taro a birnin Berlin, na baya bayan nan a jerin gwano na nuna goyon bayan jama’a ga shugaban na Ukraine daga kawayen kasashen Turai, a daidai lokacin da Kyiv ke fuskantar matsin lamba daga Washington kan ya rattaba hannu kan shirin samar da zaman lafiya wanda tun farko ya goyi bayan manyan bukatun Moscow.

KU KARANTA KUMA: Ukraine Ta Shirya Sabon Shirin Zaman Lafiya, Ta Ki Amincewa da Batun Filaye

Birtaniya, Faransa da Jamus sun yi aiki a cikin ‘yan makonnin da suka gabata don daidaita shawarwarin Amurka, wanda a cikin daftarin da aka bayyana a watan da ya gabata, ya yi kira ga Kyiv da ya ba da wasu yankuna, ta yi watsi da burinta na shiga kungiyar NATO da kuma amincewa da iyaka kan dakarunta.

Merz ya fada a cikin wani jawabi da ya yi a jiya Asabar cewa, dole ne Turai ta jajirce wajen samun sauyi a dangantakarta da Amurka yayin da take fuskantar barazana daga Rasha.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, bayan ganawarsa da shugaban Rasha Vladimir Putin, ya ce zaman lafiya bai yi nisa ba, kuma yana fatan tattaunawa da Trump kan shirin zaman lafiya.

Rasha ta kai hari kan wasu tashoshin jiragen ruwa biyu na Ukraine a ranar Juma’a Da ta gabata, inda ta lalata jiragen ruwa uku mallakar Turkiyya ciki har da wani jirgin da ke dauke da kayan abinci, kamar yadda jami’an Ukraine da wani mai jirgin ruwa ya bayyana, kwanaki bayan Moscow ta yi barazanar katse Ukraine daga teku.

 

Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos

 

Comments are closed.