Take a fresh look at your lifestyle.

NAQS Ta Koyawa Manomi Ayyukan Noma A Yankin Kudu Maso Yamma

0 22

A kokarin da ake na bunkasa noma a Najeriya tare da bunkasa kwarewar manoman yankin Kudu maso Yamma, Hukumar Kula da Kare Aikin Noma ta Najeriya (NAQS) da Arajek Multi Services Ltd, sun hada kai don shirya wani horo da ya mayar da hankali kan inganta dabarun noma musamman na masara, Ayabar plantain, da noman dabino a jihar Oyo.

 

An zabo manoma 100 daga kowace jiha a tsanake don halartar wannan taron horarwa. Taron wanda ya fara a ranar Litinin a Kwalejin Kiwon Lafiyar Dabbobi da Fasaha ta Tarayya (FCAH&PT) da ke Moor Plantation, Ibadan (babban birnin Jihar Oyo), an shirya kammala shi ne a yau Litinin.

 

A jawabin shi na maraba Shugaban Kamfanin Arajek Multi Services Ltd, Mista Rahman Idris, ya jaddada gagarumin rawar da aikin noma ke takawa wajen magance muhimman al’amura da suka hada da samar da abinci, samar da ayyukan yi, da gudummawar da ake samu a cikin gida da samar da wadata.

 

Mista Idris ya yi nuni da cewa kashi 65 zuwa 75 cikin 100 na al’ummar Najeriya na taka rawar gani wajen ayyukan noma.

 

Idris ya ce: “Ba yadda za a yi mutum ba zai ci abinci a rana ba sai idan yana azumi, don haka akwai bukatar a karfafa noma a Najeriya. Muna da kasa mai kyau daga Arewa zuwa Kudu da kuma daga Yamma zuwa Gabas.”

 

Ya ba da shawarar cewa mahalarta taron su hada kai da masu hannu da shuni don cimma manufofin da aka tsara na taron.

 

Daga bisani, ya nuna godiya ga masu gudanarwa da ma’aikatan NAQS don taimakon fasaha da sauran abubuwa.

 

A lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron, Farfesa Adeboye Omole, kodinetan horaswar, ya yi tsokaci kan horon tare da jaddada muhimmancin kiyaye lokaci, mai da hankali, da kuma taka rawar gani.

 

Ya kuma mika godiyar shi ga Gwamnatin Tarayya da NAQS kan yadda suka shiga tsakani a kan lokaci wajen horar da matasa da mata ayyukan noma. Farfesa Omole ya amince da shugaban kamfanin Arajek Multi Services Limited, Honorabul Kolapo Osunsanya, bisa gudanar da aikin tare da bayar da wannan dama.

 

Misis Bello Hadijat Jumoke, wacce ta wakilci Dr. Vincent Isegbe, Kwanturolan Hukumar NAQS, ta yi maraba da mahalarta taron horaswar. Ta kuma bukace su da su yi amfani da ilimin da za su samu a lokacin horon don ganin cewa sun yi anfani da shi.

 

 

 

Agro Nigeria / Ladan Nasidi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.