Shugabannin kasashen Rasha da Koriya ta Arewa sun gana a wata cibiyar harba makamin roka na kasar Siberiya mai nisa, inda suka fara wani taro da ka iya ganin shugabannin sun kulla yarjejeniyar makamai da za ta bijirewa takunkumin da aka kakaba mata a duniya.
Mutanen biyu sun fara ganawar tasu ne da rangadin harba makamin roka samfurin Soyuz-2, inda shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yiwa wani jami’in sararin samaniyar kasar Rasha tambayoyi game da rokokin.
Ganawar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya zo ne sa’o’i bayan da Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami guda biyu zuwa teku, wanda ya kara tunzura a gwajin makaman Koriya ta Arewa tun farkon shekarar 2022, yayin da Kim ya yi amfani da karkatar da hankalin da yakin Putin ya haifar a kan Ukraine domin kara tunzura shi inganta makamai.
Hafsan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu ba su bayyana kai tsaye ba har zuwa lokacin da makami mai linzami na Koriya ta Arewa ya tashi. Jami’an tsaron gabar tekun Japan, sun ambato Ma’aikatar Tsaro ta Tokyo, ta ce mai yiwuwa makaman sun riga sun sauka amma har yanzu sun bukaci jiragen ruwa da su yi duba abubuwan da ke fadowa.
AP/Ladan Nasidi.
Leave a Reply