Take a fresh look at your lifestyle.

Ukraine Ta Kai Hari Da Makami Mai Linzami Kan Crimea-Rasha

0 203

Rasha ta ce Ukraine ta harba makamai masu linzami 10 da jiragen ruwa marasa matuka guda uku a wani hari da ta kai kan gidan jiragen ruwanta da ke yankin Crimea.

 

 

Harin ya haifar da wata babbar gobara a tashar jiragen ruwa na Sevastopol wanda ya yi sanadin jikkata mutane 24, in ji Rasha.

 

 

Gwamnan Moscow Mikhail Razvozhayev ya yi ikirarin cewa an kama yawancin makaman.

 

 

Rasha ta ce jiragen ruwanta guda biyu sun lalace sakamakon harbo makamai masu linzami da aka yi musu.

 

 

Hoton da Mista Razvozhayev ya raba a shafin sada zumunta na Telegram ya nuna yadda wuta ke cin wani abu da alama jirgin ruwa ne a tashar jiragen ruwa yayin da yake Magana da wayar salular shi.

 

 

A shekarar 2014 ne Rasha ta mamaye Crimea daga Ukraine ba bisa ka’ida ba.

 

 

A baya dai Ukraine ta kai hari kan Sevastopol da kuma jiragen ruwan Tekun Red Sea, amma da alama wannan yana daya daga cikin hare-haren da ta hada kai har ya zuwa yanzu, mai yiwuwa ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da yammacin duniya ke kawowa.

 

 

Bakwai daga cikin makamai masu linzamin da aka harba sun lalata dukkanin jiragen ruwa guda uku, in ji ma’aikatar tsaron kasar.

 

 

Sai dai har yanzu Ukraine ba ta ce uffan ba game da harin na Crimea.

 

 

A halin da ake ciki kuma, jiragen saman Rasha sun yi barna a tashar jiragen ruwan Izmail na kasar Ukraine da ke gabar kogin Danube.

 

 

Gwamnan yankin Odesa, Oleh Kiper, ya ce mutane shida ne suka jikkata a harin wanda ya haddasa gobara da lalata kayayyakin more rayuwa.

 

 

“An aika jirage marasa matuka a gundumar Izmail,” in ji Kiper a shafin Telegram.

 

 

“Abin takaici, an sami raunuka: an yi nadi lalacewar tashar jiragen ruwa da sauran kayayyakin more rayuwa.”

 

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *