Darakta Janar na Asusun Horar da Masana’antu (ITF), Mista Joseph Ari, ya bukaci gwamnonin jihohin Arewa 19 da su ba da fifikon ci gaban matasa ta hanyar shirye-shiryen koyon sana’o’i.
Ari ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Dutse, a lokacin da ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin Jihar Jigawa kan horar da matasa.
KU KARANTA KUMA: ITF Ta Samu Yabo Akan Inganta Al’adun Karatu
A cewar Ari, ya zama wajibi kungiyar ITF da gwamnonin Arewa (NGF) su hada kai kan shirye-shiryen horas da matasa domin ganin sun dogara da kan su, da duba halin ko in kula da zamantakewa a yankin.
“A nan ne, Manajan Daraktan Rukunin NNDC ya kira ni kan yadda Gwamnatin tarayya za ta shigo domin mu kawar da talauci a jihohin Arewa.
“Wannan yana haskaka mana fuska kuma idan ba a yi komai ba, za mu zauna a kan bam na lokaci. Saboda haka mai girma gwamna a wurin taron ku (NGF) muna rokon ku da ku ga yadda za mu hada kai domin ceto lamarin,” inji shi.
Da yake mayar da martani, Namadi ya yi alkawarin zama jakadan ITF a NGF, inda ya kara da cewa, “lokaci ya yi da gwamnoni zasu fahimci rawar da asusun ke takawa wajen magance matsalolin zamantakewa”.
Namadi, ya bayyana rashin aikin yi ga matasa a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin shi, ya kara da cewa hakkin gwamnati ne ta kula da matasa.
“Ina ganin lokaci ya yi da mu a matsayinmu na gwamnoni mu fahimci mahimmancin ITF ta fuskar magance matsalolin zamantakewa a Najeriya.
“Kuma daga cikin manyan matsalolin da na fuskanta a lokacin yakin neman zabe, akwai matasa da a koda yaushe suke fitowa suna maraba da mu a duk inda muka je.
“Abun da ke damu na a kowane lokaci shine ina tunannen wadannan mutane (matasa), dole ne mu kula da su, kuma idan ba mu yi haka ba, kamar yadda kuka ce muna zaune a kan lokaci. Ya zo ne a matsayin wani nauyi a wuyanmu na kula da matasanmu,” inji shi.
Domin magance matsalar rashin aikin yi, gwamnan ya ce gwamnatin shi ta samar da hukumar da za ta hanzarta samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar shirye-shiryen koyon sana’o’i.
“Kuma wannan ne ya sanar da matakin da muka dauka na samar da hukumar inganta rayuwar matasa ta jihar Jigawa.
“Ba wai kawai mun kafa hukumar ba ne, mun kuma yanke shawarar nemo wasu kudade na daban don ganin ta dore, mu nuna damuwarmu da jajircewarmu ga ci gaban matasa a jihar Jigawa.
“Amma ta yaya za mu bunkasa matasan mu, muna bukatar mu samar musu da kwarewa kuma mun bincika ko’ina kuma mun gano cewa abokin tarayya mafi kyau don yin hakan shine ITF,” in ji shi.
Ari ya sanya hannu a madadin hukumar ta ITF, Sakataren zartarwa na hukumar tallafawa matasa da samar da aikin yi Dr Habib Muhammad ya sanya hannu a madadin gwamnatin Jigawa.
NAN/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply