Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Tattara Kudaden Haraji Ta Jihar Neja Ta Yi Nasara A Shari’ar Ta Da Bankin Stanbic IBTC

Nura Muhammed,Minna.

0 151

Hukumar tattara kudaden haraji ta jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya , karkashin Shugabanci Muhammadu Etsu Madami ta  sami nasara bisa  hukuncin da kotun daukaka Kara karkashin Mai shari’a Richard Bala ta yanke kan dambarwar dake tsakanin bankin Stanbic IBTC Mai kula da yankin arewa ta tsakiyar Najeriya da hukumar, kan batutuwa da  suka shafi kudaden haraji.

 

Kotun dai ta baiwa hukumar nasara ne bisa rashin kwararan hujjoji da ta ce bankin ya kasa gabatar mata, wanda hakan ya sanya ta bayyana hukumar a matsayin wace ta yi nasara a shari’ar.

 

Har ila yau, mai shari’a Richard Bala ya kuma kawo karshen takaddama tsakanin bangarorin biyu da ya shafi PAYE wato Pay-As-You-Earn na haraji da suka kai N54,245,812 na shekara ta 2018 da 2020 da Kuma wasu takaddamar na kudi N6,395,447,40k na shekara ta 2011 da 2021.

 

Wadanda takaddamar da suka bullo ya Sanya hukumar shigar da Kara, Wanda suka hada da kin amincewar bankin na gyra tsarin NORA da sauran batutuwa.

 

Kotun dai ta bayana cewar hukumar tattara kudaden harajin nada damar daukan wannan matakin da ta dauka musamman a bangaran kudaden haraji, inda  bisa rashin kwararrun hujjoji da bankin ya kasa kawowa, kotun ta Kori karar.

 

Wannan nasarar da hukumar ta samu ya bayana irin kokarin da Shugaban hukumar Muhammad Etsu Madami ke Yi na inganta ayyukan tun lokacin da ya hau karagar Shugabanci hukumar a shekara ta 2021.

 

Inda a tsawon lokacin da ya kwashe an sami karin kudaden shiga, musamman wajan yin anfani da tsarin nan na ITAS inda aka sami tushewar wasu kafofin da kudade ke zurarewa.

 

Wanda wannan shari’a ta nuna Karara yadda Shugaban ya himmatu wajan kawo sauyi a bangaran kudaden harajin jihar Neja ta hanyar ganin an sami cigaba ta fanin.

 

 

Nura Muhammed,Minna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.