Kasar Rasha ta yi kira da a dakatar da fada cikin gaggawa a Nagorno-Karabakh, inda Azabaijan ta kaddamar da farmakin soji kan dakarun ‘yan aware bayan shafe watanni ana tashe-tashen hankula.
An bayar da rahoton mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu fiye da 200 a fadan da ya barke ranar Talata a lokacin da Azabaijan ta aike da dakaru dauke da manyan bindigogi kan ‘yan aware a yankin Nagorno-Karabakh da ke karkashin Armeniya a yankin Kudancin Caucasus.
Nagorno-Karabakh a duk duniya an amince da shi a matsayin yankin Azarbaijan amma wani yanki nasa yana karkashin ikon hukumomin Armeniya masu neman ballewa wadanda suka ce mahaifarsu ce ta asali.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fada a jiya Laraba cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya na Rasha 2,000 a Nagorno-Karabakh suna kwashe fararen hula tare da ba da agajin jinya a cikin fadan.
“Muna kira ga bangarorin da ke rikici da juna da su gaggauta dakatar da zubar da jini, dakatar da tashin hankalin fararen hula,” in ji ma’aikatar cikin wata sanarwa.
Kasashen Amurka da Faransa sun kuma bukaci Azarbaijan ta dakatar da kai farmakin da take kai wa ‘yan awaren Karabakh a ranar Talata, inda suka ce mutane 27 da suka hada da fararen hula 2 ne aka kashe tare da jikkata wasu fiye da 200.
ALJAZEERA/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply