Take a fresh look at your lifestyle.

Hukuma Ta Kaddamar Da Shirin Rijistar Haihuwa Ta Yanar Gizo Ga Yara

1 150

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ta kaddamar da shirin rijistar haihuwa ta yanar gizo ga yara tun daga haihuwa har zuwa shekara 17, a sassan mazabu 147 da ke jihar Nasarawa. Kamfen din na hadin gwiwa ne da hukumar kidaya ta kasa NPC.

 

 

 

KU KARANTA KUMA: Uwargidan gwamnan jihar Legas ta fara shirin ga mata domin haihuwa da yawa

 

 

 

Daraktar Hukumar NOA ta Jihar Nasarawa, Dakta Priscilla Gondualor, a lokacin da take jawabi a wajen bikin ranar Alhamis a Lafiya, ta ce hukumar na hada hannu da sarakunan gargajiya domin fadakar da jama’a kan bukatar yin rijistar haihuwa.

 

 

 

A cewarta, rijistar haihuwa wani tushe ne na yin kidayar jama’a da ta dace domin baiwa gwamnati a dukkan matakai damar samar da isassun abubuwan da suka shafi ilimi, lafiya, wasanni da sauran ababen more rayuwa ga jama’a.

 

 

 

Gondualor ya ce cibiyoyin gwamnati da dama, musamman makarantu da asibitoci sun cika makil saboda rashin cikakken adadin yawan al’umma da za su jagoranci gwamnati wajen samar da isassun kayayyaki.

 

 

 

“Yana da matukar muhimmanci a yi rijistar yara a lokacin haihuwa domin baiwa gwamnati a dukkan matakai damar tsara yadda ya kamata ga ‘yan kasa. Muna da sarakunan gargajiya masu tasiri da mutuntawa, wadanda ake sa ran a tsarinsu na gargajiya su jagoranci jama’a don wayar da kan iyaye, da masu kula da su a samar da ‘ya’yansu domin yin rajista,” inji ta.

 

 

 

Ta kuma yi bayanin cewa ma’aikatan NPC za su kasance a dukkan rumfuna  na tsawon makonni uku masu zuwa a fadin jihar domin tabbatar da rajistar yara tun daga haihuwa zuwa shekaru 17.

 

 

 

Alhaji Ahmad-Yahaya Doma, Daraktan NPC na jiha ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da damar da hukumar ta ba su wajen yi wa ‘ya’yansu rajista kyauta.

 

 

 

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Lafiya, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Nasarawa, Mai shari’a Sidi Bage, ya kuma jaddada muhimmancin yin rijistar haihuwa a matsayin wani muhimmin makami da zai bai wa gwamnati damar yin tsari mai inganci ga al’umma.

 

 

 

Sarkin ya ba da tabbacin cewa cibiyar gargajiya za ta taimaka wajen tabbatar da nasarar aikin. Ya bukaci sauran sarakunan gargajiya da hakiman kauyuka da na gundumomi a fadin jihar da su kai sakon zuwa yankunan su.

 

 

 

“Mun ba ku kalamanmu, za mu yi iya bakin kokarinmu ta hanyar amfani da tsarin da muke da shi, tun daga hakimin gundumar, hakimin kauye har mai unguwa. Za mu wayar da kan su, za mu umarce su da su zurfafa domin aiwatar da wannan muhimmin sako,” inji shi.

 

 

 

NAN/ Ladan Nasidi.

One response to “Hukuma Ta Kaddamar Da Shirin Rijistar Haihuwa Ta Yanar Gizo Ga Yara”

  1. Unquestionably believe that which you said. Your favorite justification appeared to be on the web the easiest thing to be aware of. I say to you, I definitely get annoyed while people consider worries that they just don’t know about. You managed to hit the nail upon the top and also defined out the whole thing without having side-effects , people could take a signal. Will likely be back to get more. Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *