Wasu da suka tsira da rayukansu a birnin Derna na kasar Libya, sun yi ta kokawa kan neman kayayyakin more rayuwa, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye kasar a farkon watan nan.
Yayin da yawancin mazauna birnin da ke gabar tekun suka tsere daga ƙasar, wasu sun tsaya don taimakawa a ayyukan binciken, amma da ƙarancin albarkatu.
Shoukry Mohamed wanda ya tsira da ransa ya ce har yanzu akwai matsaloli da dama a garin da suka hada da matsalar wutar lantarki da ruwan sha, lamarin da ya sa shi da iyalansa suka rasa matsugunansu.
Yayin da yawancin mazauna birnin da ke gabar tekun suka tsere daga ƙasar, wasu sun tsaya don taimakawa a ayyukan binciken, amma da ƙarancin albarkatu.
Mansour Selim, wanda ke da manyan kantuna uku a cikin birnin ya garzaya a cikin kayansa don samun damar sake buɗewa da yi wa mutane hidima.
Selim ya ce “Suna son a bude kasuwanni, akwai bukatar kayayyakin kasuwa a yanzu, don haka mun yi wa jama’a hakan.”
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya janyo mummunar ambaliya a gabashin Libya a farkon wannan wata. Guguwar ta mamaye madatsun ruwa guda biyu a cikin sa’o’i na farko na ranar 11 ga watan Satumba, inda ta tura katangar ruwa mai tsayin mita da yawa a tsakiyar birnin Derna, tare da lalata daukacin unguwanni tare da share mutane zuwa teku.
Ambaliyar ta mamaye kusan kashi daya bisa hudu na birnin, kamar yadda jami’ai suka bayyana. Dubban mutane ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka mutu a karkashin baraguzan ginin ko kuma a cikin teku, a cewar kungiyoyin bincike. Jami’an gwamnati da kungiyoyin agaji sun bayar da adadin wadanda suka mutu daban-daban daga kusan 4,000 zuwa sama da 11,000.
Akalla mutane 40,000 ne suka rasa matsugunansu a yankin, ciki har da 30,000 a Derna, a cewar hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya. Mutane da yawa sun ƙaura zuwa wasu biranen ƙasar ta Libiya, waɗanda al’ummomin yankin suka karɓi baƙuncinsu ko kuma suna mafaka a makarantu.
Hukumomin yankin sun ce sun ware wani yanki mafi muni na Derna da ya lalace a yayin da ake kara nuna damuwa game da yiwuwar kamuwa da cututtuka ta ruwa.
Hukumomin lafiya sun kaddamar da wani kamfen na rigakafi wanda da farko ya nufi kungiyoyin bincike da ceto tare da yara a Derna da sauran wuraren da abin ya shafa.
Labaran Afirka / Ladan Nasidi.
Leave a Reply