Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai gana da abokin karawarsa Ilham Aliyev a ranar Litinin, yayin da dubban ‘yan kabilar Armeniya suka tsere daga Nagorno-Karabakh bayan da Azarbaijan ta fatattaki mayakan yankin a makon jiya.
Erdoğan zai kai ziyarar kwana guda a Nakhchivan na Azarbaijan mai cin gashin kan shi, wani yanki na Azeri da ke tsakanin Armenia, Iran da Turkiyya domin tattauna wa da Aliyev halin da ake ciki a yankin Karabakh, in ji ofishin shugaban Turkiyya.
Armeniyawa na Karabakh, yankin da duniya ta amince da shi a matsayin wani bangare na Azarbaijan amma a baya ya wuce ikonsa, an tilastawa tsagaita bude wuta a makon da ya gabata bayan wani samamen da sojojin Azabaijan suka yi na tsawon sa’o’i 24.
A ranar Lahadin da ta gabata, shugabannin Nagorno-Karabakh sun ce Armeniyawa 120,000 na yankin ba sa son zama a matsayin wani bangare na Azarbaijan saboda tsoron tsanantawa da kawar da kabilanci suka fara ficewa daga yankin.
Tun da misalin karfe 5 na safe (0100 agogon GMT) a ranar Litinin, sama da mutane 2,900 ne suka tsallaka zuwa Armenia daga Nagorno-Karabakh, in ji gwamnatin Armeniya a cikin wata sanarwa.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
fantastic publish, very informative. I’m wondering why the other specialists of this sector do not understand this. You should proceed your writing. I am sure, you’ve a great readers’ base already!