Amurka Ta Amince Da Tsibirin Cook A Matsayin Kasa Mai Cin Gashin Kanta – Biden
Amurka ta amince da tsibirin Cook a matsayin kasa mai cin gashin kanta, in ji sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a wata sanarwa a ranar Litinin.
Biden ya fada a cikin wata sanarwa cewa Washington ta amince da su a matsayin “jahohi masu cin gashin kansu kuma za su kulla huldar diflomasiyya da su, ya kara da cewa matakin zai taimaka wajen ciyar da yankin Indo-Pacific mai ‘yanci da bude baki.”
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Biden ke shirin yin maraba da shugabanni zuwa birnin Washington don halartar taron koli na kwanaki biyu na Amurka da tsibirin Pacific da ake sa ran zai mai da hankali sosai kan tasirin sauyin yanayi.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply