Take a fresh look at your lifestyle.

Maulud Nabi: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Taya ‘Yan Najeriya Murna

1 201

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Hon. Benjamin Okezie Kalu ya taya al’ummar Musulmi a fadin duniya murnar zagayowar wannan shekara ta Eid-il-Maulud, wanda ke tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

 

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa (CPS) Mista Levinus Nwabughiogu ya fitar, Kalu ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi koyi da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam tare da nuna soyayya ga juna musamman mabukata a cikin al’umma.

 

Mataimakin shugaban majalisar ya kuma bukaci mabiya addinin musulunci da ma daukacin al’ummar Najeriya da su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tare da yin addu’a ga ci gaban kasar nan, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba.

 

Karanta Haka: Eid-El-Maulud: VP Shettima Yana Taimakawa Musulmai

 

Kalu ya kara da cewa “Majalisar wakilai karkashin jagorancin Rt. Hon. Abbas Tajudeen yana aiki ne kan wasu dokoki da za su inganta tattalin arziki da rayuwar ‘yan Najeriya”, inda ya bukaci jama’a da kada su gaji da fatan samun makoma mai kyau.

 

Mataimakin shugaban majalisar ya yi wa daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Idin Maulud.

 

 

Ladan Nasidi.

One response to “Maulud Nabi: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Taya ‘Yan Najeriya Murna”

  1. I believe everything wrote made a lot of sense. However, what about this? what if you typed a catchier post title? I am not saying your content isn’t good., but suppose you added a post title that grabbed a person’s attention? I mean %BLOG_TITLE% is a little boring. You ought to look at Yahoo’s front page and see how they create article titles to grab people interested. You might try adding a video or a picture or two to grab people excited about what you’ve got to say. In my opinion, it could bring your blog a little livelier.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *