Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Tattalin Arziki Ta Goyi Bayan Shirin Ci Gaba Na Shugaba Tinubu

1 111

Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ta amince da ajanda guda takwas na Shugaba Bola Tinubu, wanda ta ce shi ne jigon ci gaban Najeriya.

Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban kasa a karshen taron majalisar na wannan watan, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya jagoranta.

Ya ce: “Taron ya yaba da dukkan ajandar guda takwas na Shugaba Bola Tinubu da kuma shirin sa na zuba jari a duniya da kuma matakan da ya dauka zuwa yanzu.”

Ministan ya ce majalisar ta gamsu da hadin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin tsakiya da na jihohi a Najeriya, kuma ta shawarci kananan hukumomin kasar da su yi la’akari da damammaki da a yanzu ya mamaye bangaren makamashi kamar yadda sabuwar dokar samar da wutar lantarki ta yi.

Musamman taron ya amince da cewa ya kamata a aiwatar da muhimman kudurori tare da hadin gwiwa tsakanin Jihohi da Gwamnatin Tarayya.

“Daya daga cikin kudurorin da aka bayyana shi ne isar da makamashi don ci gaban tattalin arziki mai dorewa, ya kamata gwamnati a dukkan matakai su inganta kaura daga manyan ayyukan masana’antu daga burbushin man fetur zuwa ababen more rayuwa na iskar gas tare da amincewa da cewa sabuwar dokar samar da wutar lantarki ta baiwa Jihohi da daidaikun jama’a damar shiga a dama da su. dukkan sassan bangaren makamashi,” inji shi.

Bagudu ya jaddada cewa an karfafa gwiwar gwamnatocin Jihohi da su gudanar da binciken makamashi domin tantance bukatunsu na makamashi tare da lalubo hanyoyin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu bisa ga fa’idar da suke da ita.

 

One response to “Majalisar Tattalin Arziki Ta Goyi Bayan Shirin Ci Gaba Na Shugaba Tinubu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *