Take a fresh look at your lifestyle.

0 84

Akalla mutane 10 ne suka jikkata lokacin da jami’an tsaron Indiya suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma sanduna wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suke kokarin shiga gidan babban ministan jihar Manipur, inda suka bijirewa dokar hana fita, in ji wani babban jami’in ‘yan sanda.

 

 

Wani jami’in ‘yan sanda ya ce lamarin ya yi matukar ta’azzara, bayan da a ranar Laraba wasu gungun ‘yan ta’adda dauke da makamai suka lalata ofishin jam’iyyar siyasa mai mulki tare da jefa bama-baman mai a wasu wuraren ‘yan sanda guda biyu.

 

 

Rikicin kabilanci ya jefa jihar Arewa maso Gabas mai iyaka da Myanmar cikin abin da masana harkokin tsaro da dama suka bayyana a matsayin yakin basasa da aka gwabza kan filaye da ayyukan yi da kuma siyasa tsakanin manyan kungiyoyin biyu na cikin gida.

 

 

Duk da haka, N. Biren Singh ko danginsa ba su kasance a cikin gidan a babban birnin jihar Imphal a lokacin ba, in ji babban jami’in ‘yan sanda a Manipur.

 

 

“Halin da ake ciki yana da wuyar gaske… Mutane suna karya dokar hana fita kuma an tilasta mana mu yi amfani da karfi don dakatar da su,” in ji jami’in bisa sharudan boye sunansa.

 

 

Hukumomin kasar sun ayyana dokar ta-baci a Imphal da wasu yankunan Manipur bayan da dalibai sama da 80 suka jikkata a rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar adawa da zargin sace wasu dalibai biyu da kuma kashe su.

 

 

An dakatar da ayyukan intanet na wayar hannu a jihar na tsawon kwanaki biyar.

 

 

Tun bayan barkewar rikicin a ranar 3 ga Mayu, an kashe mutane sama da 180 sannan sama da 50,000 sun tsere daga gidajensu a Manipur.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *