Take a fresh look at your lifestyle.

Afganistan Ta Dakatar Da Ayyukan Ofishin Jakadancin Indiya

1 118

Ofishin jakadancin Afganistan da ke Indiya ya dakatar da dukkan ayyukansa bayan da jakadan da wasu manyan jami’an diflomasiyya suka bar kasar zuwa Turai da Amurka inda suka samu mafaka, in ji jami’an ofishin jakadancin uku.

 

Indiya ba ta amince da gwamnatin Taliban ba kuma ta rufe ofishin jakadancinta a Kabul bayan da Taliban ta karbe iko a 2021.

 

Sai dai kuma New Delhi ta baiwa jakada da ma’aikatan mishan da gwamnatin hambararren shugaban Afganistan Ashraf Ghani ke marawa baya ta nada don ba da biza da gudanar da harkokin kasuwanci.

 

A halin da ake ciki, akalla jami’an diflomasiyyar Afghanistan biyar sun bar Indiya, in ji jami’an ofishin jakadancin. A yanzu gwamnatin Indiya za ta karbe ofishin diflomasiyya a matsayin na wucin gadi, in ji daya daga cikin jami’an Afghanistan.

 

Rahoton ya ce jami’an ma’aikatar harkokin wajen Indiya a New Delhi sun ce suna duba abubuwan da ke faruwa, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

 

Jami’an Taliban a Kabul ba su kai ga samun karin bayani ba.

 

Indiya tana ɗaya daga cikin ƙasashe goma sha biyu waɗanda ke da ƙaramin aiki a Kabul don sauƙaƙe kasuwanci, taimakon jin kai, da tallafin magunguna. Kasuwancin kasashen biyu a shekarar 2019-2020 ya kai dala biliyan 1.5 amma ya fadi sosai bayan da gwamnatin Taliban ta karbi mulki.

 

A farkon wannan watan daruruwan daliban jami’ar Afganistan da ke zaune a Indiya duk da karewar takardar izinin dalibansu sun gudanar da zanga-zanga a birnin New Delhi domin neman gwamnatin Indiya ta tsawaita zamansu.

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

One response to “Afganistan Ta Dakatar Da Ayyukan Ofishin Jakadancin Indiya”

  1. I’m truly enjoying the design and layout of your website. It’s a very easy on the eyes which makes it much more enjoyable for me to come here and visit more often. Did you hire out a developer to create your theme? Exceptional work!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *