Firaministan Sweden ya ce nan ba da dadewa ba sojoji za su taimaka wa ‘yan sanda da wasu ayyuka don taimakawa wajen shawo kan matsalar laifuffukan da ba a taba gani ba wanda ya girgiza kasar Scandinavia da kusan kullum ana harbe-harbe da tashin bama-bamai.
Firayim Minista Ulf Kristersson ya ce gwamnatinsa ta dama za ta ba da sanarwar ranar Alhamis mai zuwa kan yadda sojojin za su yi aiki da ‘yan sanda.
Shugaban ‘yan sandan kasar, Anders Thornberg, ya fayyace a safiyar Juma’a cewa ba za a bai wa jami’an rundunar ‘yan sanda aikin ‘yan sanda kai tsaye ba.
“‘Yan sanda ba za su iya yin dukkan ayyukan da kansu ba,” in ji Kristersson bayan wani taro da shugabannin sojojin da ‘yan sandan kasar.
Firayim Ministan ya lura cewa sojojin kasar sun riga sun shagaltu da tabbatar da shiri saboda yakin da ake yi a Ukraine. Sai dai ya ce watakila sojojin na iya taimakawa ‘yan sandan kasar da sanin ababen fashewa, jiragen sama masu saukar ungulu, da nazari, kuma ana iya yin hakan a cikin dokokin kasar da ake da su.
Rahoton ya ce Sweden ta kwashe shekaru tana fama da tashe tashen hankula, amma yawan harbe-harbe da tashin bama-bamai a watan Satumba ya banbanta.
An kashe mutane uku a cikin ‘yan kwanakin nan a wasu hare-hare daban-daban da ake zargin suna da alaka da gungun masu aikata laifuka, wadanda galibi ke daukar matasa a unguwannin bakin haure marasa galihu don kai hari.
A halin da ake ciki kuma, Kristersson ya ce akwai bukatar a tsaurara dokokin kasar Sweden domin dakile daukar matasa aiki cikin kungiyoyin, kuma ya yi imanin cewa akwai rinjaye a majalisar dokokin kasar Sweden domin yin sauye-sauyen da suka dace.
Fiye da mutane 60 ne suka mutu sakamakon harbe-harbe a shekarar da ta gabata a Sweden, adadi mafi girma da aka samu. Wannan shekara tana kan hanya ta zama iri ɗaya ko mafi muni. Hukumomin kasar dai sun danganta bullar tashe-tashen hankula na baya bayan nan da takun saka tsakanin bangarorin da ke gaba da juna na kungiyoyin masu aikata laifuka na kasa da kasa.
AP/Ladan Nasidi.
Leave a Reply