Take a fresh look at your lifestyle.

Kakakin Majalisa Ya Koka Da Sace Dalibai

0 339

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Abbas Tajudeen ya koka kan yadda wasu ‘yan bindiga suka sake sace dalibai a manyan makarantu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shugaban Majalisar ya bayyana damuwarsa ne biyo bayan tabbatarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Larabar da ta gabata kan sace wasu dalibai biyar na jami’ar tarayya da ke Dutsinma a jihar.

Da yake mayar da martani game da sace daliban, shugaban majalisar Abbas ya yi kira ga jami’an tsaro da su kubutar da daliban da aka sace, tare da hana afkuwar lamarin, inda ya ce sace daliban na da matukar barazana ga ilimi a Arewa da ma ko ina a fadin kasar nan.

Da yake bayyana irin wannan mugunyar dabi’ar, Kakakin Majalisar Abbas, ya bukaci sojoji da hukumomin tsaro da su gaggauta gyara gine-ginen su da hanyoyin tabbatar da tsaron dukkan ‘yan Nijeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummomin da ke karbar bakuncin manyan makarantun da su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar yin taka tsantsan da kuma kai rahoton duk wani motsi da ake da su a yankunansu.

Idan za a iya tunawa, a ranar 22 ga Satumba, 2023, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki a wasu gidajen kwanan dalibai mata guda uku a yankin Sabon Gida a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai mata da ba a tantance adadinsu ba a Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUG).

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *