Biden Zai Karbi Bakuncin Shugaban Jamus A Fadar White House
Shugaban Amurka Joe Biden zai gana da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a fadar White House ranar Juma’a don tunawa da ranar Jamus da Amurka, inji fadar White House.
Shugabannin biyu za su sake jaddada alakar su, “ciki har da hadin gwiwarmu ta kut-da-kut a matsayin kawancen kungiyar tsaro ta NATO kan wasu muhimman batutuwa kamar kare martabar dimokiradiyya da kuma kudurin mu na goyon bayan Ukraine yayin da take kare kanta daga mamayar Rasha.”
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply