Take a fresh look at your lifestyle.

Yakin Isra’ila-Hamas: Isra’ila Ta kai Hare-Haren Ba Sani Ba Sabo A Zirin Gaza

0 185

Isra’ila ta kai hari a zirin Gaza da a cikin dare na biyu a jere bayan ayyana yaki a hukumance kan kungiyar Hamas ta Falasdinu.

 

 

Rundunar sojinta ta ce wasu dakaru 100,000 ne suka taru a kusa da Gaza.

 

 

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin ‘yan bindigar Hamas da sojojin Isra’ila a akalla yankuna uku a Kudancin Isra’ila, ciki har da kibbutz a Karmia da kuma garuruwan Ashkelon da Sderot.

 

 

Gabanin yuwuwar mamayar Isra’ila a Gaza, Tarek Abu Azzoum na Al Jazeera, wanda ke yankin Kudancin Falasdinu, ya ba da rahoton cewa, a cikin sa’a na karshe, yankin Beit Hanoun ya kasance cikin mummunan tashin bama-bamai daga iska.

 

 

 

“Mataki da saurin da ake kai hare-hare ta sama a cikin zirin Gaza ya karu matuka a cikin sa’o’i biyun da suka gabata,” ya kara da cewa an kai wasu gine-ginen ba tare da gargadi ba.

 

 

“Ba a san takamammen asarar rayuka ba saboda gazawar jami’an agajin gaggawa na isa yankin.”

 

 

Adadin wadanda suka mutu na baya-bayan nan ya kai Falasdinawa 413, a cewar Jami’an lafiya.

 

 

Harin ba-zata na Hamas ya zo ne bayan da Isra’ilawa ‘yan ci-rani suka mamaye harabar masallacin Al-Aqsa a cikin ‘yan kwanakin nan kuma Isra’ila ta kashe Falasdinawa da dama a ‘yan watannin nan.

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *