Take a fresh look at your lifestyle.

An kama Shugaban Babban Bankin kasar Burundi Daga Mukamin Shi Bisa Laifin karkatar Da Kudade

0 145

An kama gwamnan babban bankin kasar Burundi da aka kora bisa zargin karkatar da kudade da kuma karkatar da kadarorin jama’a.

 

Laifukan da ake tuhumar Dieudonné Murengerantwari “na wucin gadi ne” da ake jiran sakamakon bincike, in ji ma’aikatar shari’a.

 

Har yanzu Mista Murengerantwari bai mayar da martani kan zargin ba.

 

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasar Burundi Évariste Ndayishimiye ya kore shi daga mukaminsa, kusan shekara guda bayan ya hau kan mukamin.

 

Tattalin arzikin kasar Burundi na cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kudaden kasashen waje da ya sanya aka samu wahalar shigo da kayayyaki.

 

A shekarun baya-bayan nan ma ta fuskanci karancin man fetur daga lokaci zuwa lokaci, da hauhawar farashin kayayyaki wanda ya kara tabarbarewar tsadar rayuwa.

 

Kusan kashi 65 cikin 100 na al’ummar miliyan 12 na fama da talauci, a cewar bankin duniya.

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar shari’a ta zargi Mista Murengerantwari da “kulasa tsarin tafiyar da tattalin arzikin kasa yadda ya kamata, cin hanci da rashawa, karkatar da kudade da kuma karkatar da kadarorin jama’a”.

 

Ba ta bayar da wani karin bayani ba, amma babban lauyan gwamnati Leonard Manirakiza ya ce tsohon gwamnan zai ci gaba da zama a gidan yari yayin da ake ci gaba da bincike.

 

An nada Mista Murengerantwari a kan wannan mukami – wanda ke da matukar muhimmanci wajen samun daidaiton tattalin arziki – tsawon shekaru biyar, amma an kore shi a shekara ta biyu a kan karagar mulki.

 

A baya ya kasance babban daraktan bankin raya kasa mai alaka da gwamnatin Burundi.

 

An maye gurbinsa da wani memba na hukumar bankin, Édouard Normand Bigendako.

 

Mista Murengerantwari shi ne shugaban babban bankin Afirka na biyu da ya fuskanci matsalar shari’a a bana.

 

An dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a watan Yuni, sannan kuma an tuhumi shi da laifin mallakar bindiga da harsashi ba bisa ka’ida ba. Ya musanta zargin.

 

 

BBC/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *