Take a fresh look at your lifestyle.

An Yi Wata Girgizar kasa Ta A Yammacin Afghanistan

0 135

Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta afku a lardin Herat na yammacin kasar Afganistan a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya tilastawa Hukumomin kasar sake tura tawagar agaji da ceto wadanda tuni suka shiga cikin filin bayan wasu munanan girgizar kasar da aka yi a ranar Asabar.

 

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan hasarar rayuka, in ji kakakin hukumar kula da bala’o’i Janan Sayeeq, amma jami’an lardin sun ce an lalata daruruwan gidaje.

 

Ofishin Gwamnan Herat ya ce wasu yankunan sun yi “asara mai yawa”, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

 

“Kungiyoyin likitocin tafi-da-gidanka da jami’ai suna aiki tare kuma sun tura wasu da suka jikkata zuwa asibiti,” in ji ofishin gwamnan a cikin wata sanarwa.

 

Girgizar kasar ta ranar Asabar ta kashe akalla mutane 2,400 tare da raunata fiye da 2,000, in ji gwamnati, wanda ya sa girgizar kasar ta kasance mafi muni a duniya a bana.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *