Harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 2,450 tun bayan harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila a makon jiya, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Ma’aikatar ta kara da cewa wasu mutane 9,200 kuma sun jikkata yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama a kan yankunan da ke gabar tekun Falasdinu.
Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta shaida wa BBC cewa “ana tura Gaza cikin wani rami mai zurfi.”
Iran a ranar Lahadi ta yi gargadin cewa duk wani farmakin kasa da Isra’ila za ta kai a zirin Gaza zai iya fadada yakin da ake yi a wasu wurare a Gabas ta Tsakiya.
BBC/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply