A yayin da aka kidaya kusan dukkan kuri’un da aka kada a zaben Laberiya, shugaba George Weah da babban abokin hamayyar shi Joseph Boakai na ci gaba da fafatawar kunnen Doki, wanda ke nufin za su fafata a zagaye na biyu na zaben.
A halin yanzu Mista Weah yana da kashi 43.8% na kuri’un da aka kada yayin da Mista Boakai ya samu kashi 43.5%, kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna.
Dan takara na bukatar sama da kashi 50% na kuri’un da aka kada domin bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Zaben na ranar 10 ga Oktoba shi ne zaben shugaban kasa mafi kusa a Laberiya tun bayan yakin basasa shekaru ashirin da suka gabata.
Hukumar zaben ta fitar da sabon sakamakon ne bayan da aka kidaya kuri’u sama da kashi 98% na rumfunan zabe, lamarin da ya bai wa Mista Weah nasara da kuri’u 5,456.
Hukumar ta ce za a sake kada kuri’a a wasu sassan kananan hukumomin Sinoe, Nimba da Montserrado ranar Juma’a bayan da wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi magudin zabe.
Babu daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa 18 da ya samu fiye da kashi 3% a zagayen farko, kuma akwai yiwuwar manyan ‘yan takarar biyu su nemi amincewar su, domin kowace kuri’a za ta kirga a zagaye na biyu na zaben.
Mista Weah, wanda tsohon dan wasan kwallon kafa ne na duniya, na neman wa’adi na biyu a matsayin shugaban kasa.
Shugaban ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben 2017 da kashi 61.5% yayin da Mista Boakai ya samu kashi 38.5%.
Ya samu kuri’u mafi yawa a zagayen farko na wancan zaben – kashi 38.4% yayin da Mista Boakai ya samu kashi 28.8%, abin da ke nuni da cewa Mista Boakai ya yi nasara a zaben makon jiya.
Wani manazarci Abdullah Kiatamba ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa duk wanda ya zo kan gaba a zagayen farko zai samu tagomashi sosai.
Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben ne a ranar 7 ga watan Nuwamba bayan bayyana sakamakon a hukumance.
Manazarta sun ce wannan na iya zama yunkurin na karshe na neman shugabancin Mr Boakai, mai shekaru 78.
Ya taba zama mataimakin shugaban kasa a gwamnatin shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf wacce ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel saboda kokarinta na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Laberiya bayan wani kazamin yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 250.
Ya gudanar da yakin neman zabensa ne a karkashin taken “Ceto”, yana mai cewa kasar Afirka ta Yamma ta yi kasa a gwiwa a shekaru shida na farko na Mista Weah.
Mista Weah, mai shekaru 57, ya yi watsi da zargin Mista Boakai, yana mai cewa ya samu gagarumin ci gaba, ciki har da gabatar da tallafin karatu ga daliban jami’a.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply