Sassan Gabashin Scotland ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a ranar Juma’a bayan da ruwan sama kamara da bakin kwarya hade da guguwar Babet mai gudun fiye da 70 mph da tayi sanadiyar rushewar dubban gidaje da ya tsinke wutar lantarki .
Masanin hasashen yanayi na Biritaniya, Ofishin Met, ya ba da gargadi game da ruwan sama tun daga watan Fabrairun 2020, yana mai hasashen wasu wurare za su samu ambaliyar.
Rahotanni sun nuna rasuwar wata mata a ranar Alhamis bayan da aka shiga cikin kogi neman wadanda suka salwanta, yayin da ‘yan sandan Scotland suka ce a ranar Juma’a an gudanar da bincike bayan rahoton wani mutum da ya makale a cikin mota dake cikin ruwa.
Hukumar da ke karamar hukumar Angus ta bukaci sama da gidaje 400 da su fice ranar Alhamis saboda gargadin ambaliyar ruwa, kuma an rufe makarantu.
Kungiyoyin Lantarki na Scotland da Kudancin kasar sun ce suna kokarin dawo da wutar lantarki ga dubban gidaje.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply