Kusan sojojin Faransa 200 ne suka bar garin Ouallam da ke kudu maso yammacin jamhuriyar Nijar a ci gaba da ficewa daga yankin Sahel, kamar yadda gidan talabijin na Tele Sahel mallakar gwamnatin kasar ya ruwaito.
Ya ce sojojin Faransa 193 da ke Ouallam sun bar sansanin su zuwa kasar Chadi ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce sojojin sun tafi ne da manyan motoci 28 da kuma motocin yaki 24 masu sulke da sauran motocin tallafi.
Chadi ta amince da bayar da “ hanya” domin janye sojojin Faransa daga Nijar zuwa Faransa. An fara atisayen janyewar ne a ranar 5 ga Oktoba.
Faransa ta aike da sojoji kusan 1,500 zuwa Nijar don taimakawa wajen tunkarar ta’addancin masu jihadi tun shekara ta 2015.
Sojojin Faransa sun kasance a Yamai babban birnin kasar, Ouallam da Ayoru – kusa da kan iyaka da Mali.
BBC/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply