Dubban mutane ne suka rattaba hannu kan wata takardar koke ta yanar gizo inda suka bukaci a dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin Dakar da Ziguinchor, babban birnin Casamance na kudancin Senegal. Sama da watanni hudu aka dakatar da hidimar saboda rikicin siyasa da ya shafi dan adawa Ousmane Sonko.
An ƙaddamar da koken, Xavier Diatta, shugaban wani kamfanin abinci a Ziguinchor a ranar 13 ga Oktoba, ya sami sa hannun sama da 3,796 tun daga ranar Litinin, 23 ga Oktoba, 2023.
Mahukuntan Senegal sun dakatar da zirga-zirgar fasinja da jigilar kayayyaki da jiragen ruwa uku suka bayar ba tare da wani bayani a hukumance ba tun watan Yuni. Dakatarwar ta biyo bayan tarzomar da ta barke a Ziguinchor da wasu garuruwan kasar biyo bayan hukuncin da aka yanke wa dan adawar siyasar kasar Sonko a wani shari’a mai alaka da da’a.
Ma’aikatar Kamun kifi da ke sa ido kan ayyukan jiragen ruwa, da kamfanin da ke gudanar da ayyukan, Cosama (wata hukuma mai zaman kanta), ba su mayar da martani ba. Wata majiya a ma’aikatar ta bayyana cewa an dakatar da aikin ne saboda ‘dalilan tsaro.
Tun daga wannan lokacin, akwai wofi a tashar Ziguinchor. Dukkanin tattalin arzikin yankin ya tsaya cak, kuma farashin sufuri ta hanya ya ninka sau uku. Farashin kayayyakin da ke fitowa daga Dakar ma sun karu, a cewar Diatta.
Sira Mané, ’yar shekara 37 mai sayar da abinci a kusa da tashar jiragen ruwa na Ziguinchor, ta bayyana takaicinta, tana mai cewa, ‘Mun gaji. Sayar da kaya ya zama ciwon kai.’
Salif Diédhiou, mai shekaru 51 ma’aikacin jirgin ruwa, ya koka kan gazawarsa wajen yin aiki kuma ya bayyana cewa ya koma aikin kamun kifi tun da jirgin ya daina zuwa Ziguinchor.
Casamance sananne ne da kamun kifi, ‘ya’yan itatuwa, da kayan marmari, waɗanda ake jigilar su sau da yawa a mako zuwa Dakar ta hanya ko ta iska.
Bayan tarzomar watan Yuni, hukumomin Senegal sun dakatar da zirga-zirgar motocin bas zuwa yankin na wani dan lokaci. Ya zuwa yanzu dai ba a samu damar shiga jirgin ba ga mutane da dama da ke son isa wannan yanki, wanda ke fama da tawayen ‘yan aware masu dauke da makamai tun shekara ta 1982 kuma Gambiya ta raba shi da sauran kasar.
Tun a karshen watan Yuli ake tsare da dan adawa Sonko, wanda ke rike da mukamin magajin garin Ziguinchor, bisa tuhume-tuhume daban-daban da suka hada da tayar da kayar baya. A ranar Talata ne ya sanar da cewa zai koma yajin cin abinci da ya tsaya a farkon watan Satumba, domin hada kai da magoya bayansa da aka kama da ba a yi musu adalci ba.
A matsayinsa na dan takara a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2024, Sonko mai shekaru 49, ya zargi Shugaba Macky Sall, wanda ya musanta zargin, da yunkurin cire shi daga zaben ta hanyar doka.
Shugaba Sall, wanda aka zaba a shekarar 2012 kuma aka sake zabe a shekarar 2019, ya bayyana a farkon watan Yuli cewa ba zai sake neman tsayawa takara ba.
Africanews/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply